Ben White: Arsenal ta ɗauki ɗan bayan Ingila daga Brighton kan kudi £50m

An wallafa

Arsenal ta ɗauki ɗan bayan Ingila daga Ben White Brighton kan kudi £50m.

Dan wasan mai shekara 23, wanda daga bayan kocin Ingila Gareth Southgate ya kira shi tawagar kasar a gasar Euro 2020 ya amince kan kwanataragi mai tsayi a filin wasa na Emirates.

Arsenal ta amince da cinikin ne a watan jiya inda ta ce dan wasan zai koma kungiyar da zarar ya dawo daga hutu.

"Ben ne babban dan wasan damuka sa a gaba kuma abin alfaharinmu ne mun kammala cinikinsa," in ji kocin kungiyar Mikel Arteta.

"Ben dan wasa ne mai hazaƙa da basira wanda yake samun nutsuwa in kwallo na kafarsa, tsarin kwallonsa zai yi daidai da namu.

"Bugu da kari yaro ne mai jini a jika, shekarunsa sun yi daidai da abin da muke so domin gina kungiyarmu. Muna shirin mayar da Ben babban dan wasanmu na tsakiya nan gaba."

Sauya sheƙar da ɗan wasan ya yi, ya kawo karshen zagayen da ya jima yana yi na kungiyoyi, a bayan Southampthon ta sake shi yana ɗan shekara goma sha, kafin daga bisani Brighton ta dauke shi a 2016.

Ya daɗe a matsayin aro a kungiyar Newport da Peterborough kafin ya koma Leeds wadda ta dauki Championship a 2019-20 duka a matsayin aro.

White shi ne dan wasa na uku da Arsenal ta dauka a wannan kakar, bayan zuwan dan wasan tsakiya Albert Sambi Lokonga daga Anderlecht da kuma dan wasan baya Nuno Tavares daga Benfica.

White zai sanya lamba hudu a Arsenal, wadda a yanzu babu mai ita tun bayan ajiye ta da David Luiz ya yi wanda ya bar kungiyar.