Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Pogba, Martinez, Bellerin, Bailey, Vlahovic, Haaland, El Ghazi
Paris St-Germain ta somatattaunawar farko domin ganin ko Paul Pogba yana sha'awar tafiya can daga Manchester United a bazarar da muke ciki ko mai zuwa, lokacin da kwangilar dan wasan na Faransa, mai shekara 28, za ta kare. (Athletic, subscription required)
United ta fara shirin karbar tayi daga PSG kuma tana son ta sayar da Pogba a kan kusan £45m. (Eurosport)
Arsenal za ta yi musayar dan wasan Sifaniya Hector Bellerin, mai shekara 26, a wani bangare na dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23. (Football Insider)
Aston Villa ta nemi biyan euro 30m (£25.5m) kan Leon Bailey, mai shekara 23, amma Bayer Leverkusen tana son a biya ta euro 35m (£29.8m) kan dan wasan nan Jamaica, wanda kuma Leicester City da Wolvessuke zawarcinsa. (Bild - in German)
Tottenham tana son daukar Dusan Vlahovic dagaFiorentina, wadda za ta nemi a biya ta kusan £50m dan dan wasan na Serbia, mai shekara 21. (Telegraph)
Dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21, da dan wasan Jamus Julian Brandt, mai shekara 25, za su ci gaba da murza leda a Borussia Dortmund a bazarar nan. (Tuttosport - in Italian)
Ajax ta tabbatar da cewa Arsenal da Lyon sun nuna sha'awar aukar golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 25, wanda aka dakatar daga wasa saboda shan kwayoyin kara kuzari. (Voetbal International, via Sun)
Norwich City na shirin mika £10m ga PAOK Salonika kan dan wasan Girka mai shekara 19 Christos Tzolis. (Football Insider)
Barcelona ba ta amince kan sabuwar kwangila da Ilaix Moriba ba, dan wasan Sifaniya mai shekara 18, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara mai zuwa kuma kungiyoyin Gasar Firimiya suke rububinsa. (Marca)
Aston Villa za ta bari dan wasan Netherlands Anwar El Ghazi, mai shekara 26, ya tafi idan Roma ta biya ta £15m kan dan wasan . (Football Insider)
Juventus za ta sake ganawa da jami'an Sassuolo inda take fatan kammala yarjejeniyar daukar dan wasan Italiya Manuel Locatelli, mai shekara 23, kuma take son sayen dan wasan Brazil Kaio Jorge, mai shekara 19, dagaSantos. (Tuttosport - in Italian)