Erling Braut Haaland: Borussia Dortmund ba za ta sayar da Haaland ba

An wallafa

Borussia Dortmund ta ce ba za ta sayar da Erling Braut Haaland ba a bana, bayan da Chelsea ke son daukar dan kwallo.

BBC ta fahimci cewar Chelsea ba ta taya dan kwallon ba, wanda zai cika shekara 21 ranar 21 ga watan Yuli.

Kocin Chelsea, Thomas Tuchel na son salon taka ledar Haaland, wanda ya ci kwallo 20 a wasa 16 a Champions League a Red Bull Salzburg da kuma Borussia Dortmund.

Shima kocin Manchester City, Pep Guardiola na bibiyar dan wasan.

Guardiola dan kasar Sifaniya, na neman mai cin kwallayen, bayan da Sergio Aguero ya koma Barcelona, wanda yarjejeniyarsa ta kare a Etihad a bana.

Ana kuma alakanta City da cewar tana son yin zawarcin dan wasan Ingila, Harry Kane, wanda ake cewar zai bar Tottenham a bana.

Sai dai City ta nisanta kanta da cewar za ta dauki dan kwallon Barcelona, Antoine Griezmann da na Bayern Munich, Robert Lewandowski.

Tuni Dortmund ta ce ba za ta sayar da Haaland ba, zai ci gaba da yi mata wasanni a kakar da za a fara cikin watan Agusta.

Kungiyar ta Jamus sayar da Jadon Sancho, mai shekara 21 ga Manchester United kan fam miliyan 73 a bana.

Dortmund ta ce Sancho kadai ta amince ta sayar a bana, amma sauran 'yan wasanta za su ci gaba da taka mata leda.