Man City ta hana Rodri da Ferran zuwa gasar Olympic

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya fayyace yadda Manchester City ta hana Rodri da Ferran wakiltar Sifaniya a gasar kwallon kafa a Olympic da za a yi a birnin Tokyo a bana.
'Yan wasa shida daga tawagar Sifaniya ne ke wakiltar kasar a Euro 2020, ciki har da dan wasan Barcelona, Pedri da Eric Garcia da aka gayyata gasar Olympic da za a fara cikin watan Yuli.
Tawagar ta Sifaniya ta umarci dukkan 'yan kwallon da ta gayyata gasar Olympic da su halarci atisayen da za ta fara daga ranar 12 ga watan Yuli, kwana daya da kammala Euro 2020.
A doka kungiyoyin da ba daga cikin Sifaniya ba, suna da damar hana 'yan wasansu zuwa gasar Olympic, amma ita kuma tana barin 'yan kwallon da ke wasa a kasar su je su wakilci kasashen su.
''Ferran Torres da kuma Rodri ba za su je Olympic ba, saboda sun buga gasar cin kofin nahiyar Turai. Wasanni za suyi musu yawa,'' kamar yadda Guardiola ya sanarwa da TV3 ranar Litinin.
''Gasa daya dan wasa ya kamata ya wakilci kasarsa a kakar tamaula. Kungiyoyi ne ke biyansu albashi, saboda haka ya kamata su tsare kadarorinsu. Kakar da za a fara tana da kalubale da yawa, amma sai kirkiro wasanni ake yi.''
Tawagar Sifaniya za ta kara da ta Italiya a wasan daf da karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Talata.







