Barcelona ta dauki Memphis Depay

An wallafa

Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Memphis Depay da zarar kwantiraginsa ya kare a Olympic Lyon a karshen watan Yuni.

Dan kwallon tawagar Netherlands da ke buga mata gasar Kofin Nahiyar Turai a yanzu haka, zai saka hannu kan yarjejeniyar taka leda a Nou Camp zuwa karshen kakar 2022/23.

Depay shi ne na hudu da Barcelona ta dauka a bana bayan Sergio Aguero da Eric Garcia da kuma Emerson.

Dan wasan da aka haifa a Moordrecht ta Netherlands ranar 13 ga watan Fabrairun 1994, ya fara tamaula a kungiyar kwallon kafa ta VV Moordrecht da ke garinsu.

Yana da shekara tara da haihuwa ya koma Sparta Rotterdam, daga nan PSV Eindhoven ta dauke shi, wanda ya fara buga wa babbar gasar kasar tamaula wato Eredivisie.

Depay wanda ya samu horo karkashin tsohon dan kwallon Barcelona, Phillip Cocu, ya zama kashin baya a Eindhoven kuma fitaccen dan wasa a babbar gasar Netherlands..

Daga nan ne Manchester United ta dauke shi karkashin Louis van Gaal, wanda ya yi kaka daya da rabi, sannan ya koma Olympic Lyon a Janairun 2017.

Nan da nan ya samu shiga tawagar kwallon kafa ta Netherlands wanda ya yi wasa karkashin Ronald Koeman.

Kazalika, yana cikin 'yan wasan da suka kai kasar ta yi ta uku a gasar Kofin Duniya a 2014, kuma ya ci kwallo a gasar Nahiyar Turai da ake yi ta bana.