An hana magoya baya daga Ingila zuwa kallon wasan karshe na Champions

An wallafa

An hana magoya bayan Chelsea da Manchester City zuwa Turkiyya domin kallon wasan karshe na gasar zakarun Turai.

Sakataren harkokin sufuri Burtaniya Grant Shapps ne ya sanar da hakan, bayan sanya sunan Turkiyyan cikin jerin kasashen da aka haramta zuwa.

Wasa mafi mahimmanci a Turai wanda za a buga a Istanbul a ranar 29 ga watan Mayu.

Schapps ya ce kasashen da aka sanya sunansu cikin bakin littafi "saboda korona ba za a je cikinsu ba sai da wani kwakkwaran dalili".

Kuma ya kara da cewa gwamnati daidai take da daukar nauyin wasan a yi shi a Ingila.

Schapps yace hukumar kwallon kafa ta Ingila na tattaunawa da Uefa kan yadda za a koma da wasan Burtaniya, amma "hukuncin haka na hannun Uefa".

"Burtaniya na da tsari mai kyau na bibiyar wannan cutar ta yadda za ta iya daukar nauyin buga wasan tare da 'yan kallo, mune wurin da ya kamata a yi wasan," in ji shi.

"Dan haka kofar mu a bude take don yin hakan, amma dai ko me za a yi Uefa ke da hukuncin karshe. Amma ganin cewa duka kungiyoyin na Ingila ne shi yasa muke neman yadda za muga an bar mu."