Abin da kuke son sani kan wasan Real Madrid da Chelsea

An wallafa

Real Madrid ta ziyarci Chelsea, domin buga wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Laraba a Ingila.

A makon jiya ranar Talata Chelsea ta je ta tashi 1-1 a gidan Real Madrid a wasan farko na daf da kasrhe a Spniya.

Real ta kara da Chelsea karo hudu ba ta taba samun nasara a kan kungiyar Stamford Bridge ba, ita ce wadda Real ta kasa ci a gasar zakarun Turai.

Sun fafata a 1971 a Cup Winners Cup inda suka tashi 1-1 a wasan farko a na biyu kuwa Chelsea ta yi nasara da ci 2-1.

Sun hadu 1998 inda Chelsea ta doke Real Madrid ta kuma lashe Uefa Super Cup da ci 1-0.

Sai kuma kara a 2021 a Champions League da suka tashi 1-1 a Spaniya wasan farko na daf da karshe.

Wannan shi ne wasa na 164 a Uefa Champions League tsakanin kungiyar Ingila da ta Spaniya, inda a wasa takwas baya kungiyoyin Ingila sun yi nasara a hudu da canjaras uku da rashin nasara daya.

Wannan shi ne karo na tara da Chelsea za ta buga karawar daf da karshe a Champions League, ita kuwa Real Madrid za ta fafata ne karo na 15.

Zinedine Zidane da kuma Thomas Tuchel suna daga cikin koci 24 da suka ja ragamar wasa sama da 6tun daga zagaye na biyu a Champions League.

Kocin Chelsea, Thomas Tuchel ya fusaknci Real Madrid ba tare da rashin nasara ba a Champions League sau biyar, inda ya ci daya da canjaras hudu.

A tarihin gasar Champions League wani kocin da ya fuskanci Real sau hudu ba tare da ta yi nasara a kansa ba shi ne Gerard Houllier da ya yi nasara a biyu da canjaras biyu.