Manchester City ta ci wasa 21 a jere a dukkan fafatawa

An wallafa

Manchester City ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier League, bayan da ta doke Wolverhampton da ci 4-1 a Etihad ranar Talata.

Minti 15 da fara tamaula Wolves ta ci gida ta hannun Leander Dendoncker, yayin da Conor Coady ya farke bayan da suka koma karawar zagaye na biyu, bayan hutu kenan.

Sai dai City ta kara na biyu ta hannun Gabriel Jesus, sai Riyad Mahrez ya kara na uku, sanan Gebriel Jesus ya ci na hudu kuma na biyu a fafatawar.

Da wannan sakamakon City ta ci wasa 21 a jere a dukkan fafatawa , kuma na 28 da ba a samu nasara a kanta ba.

Rabon da a yi nasara a kan City tun ranar 21 ga watan Nuwamba, wanda Tottenham ta doke kungiyar ta Etihad da ci 2-0 a gasar Premier League.

City ta ci wasa 21 a jere tun bayan da ta tashi kunnen doki 1-1 da Wesr brom ranar 18 ga watan Disamba.

A wasa 21 da ta ci a jere har da karawa biyu a Caraboa da uku a FA Cup da cin wasan Champions League daya, sauran bajintar a Premier League ta yi.

City ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi, ta kuma bai wa Manchester United tazarar maki 15.

Ranar Laraba, Manchester United za ta je gidan Crystal Palace a gasar ta Premier League.

Kungiyar ta Etihad mai fatan lashe kofi hudu a bana ta kai wasan karshe a Carabao Cup da Quarter finals a FA ta kuma ci Gladbach a Champions League, ita ce ta daya a Premier.