Real Madrid ta koma ta uku a teburin La Liga

An wallafa

Real Madrid ta tashi 1-1 da Real Sociedad a wasan mako na 25 a gasar La Liga da suka kara a Alfredo Di Stefano Litinin.

Sociedad ce ta fara cin kwallo ta hannun Cristian Portugues, yayin da Real ta farke ta hannun Vinicius Junior daf da za a tashi daga wasan.

Vinicius ya ci kwallon ne a lokacin da ya buga wa Real Madrid wasa na 100 a kungiyar.

A karawar farko da suka yi a gasar ta Spaniya a bana tashi suka yi 0-0 a gidan Sociedad ranar 20 ga watan Satumba.

Da wannan sakamakon Real ta koma ta uku a kan teburi da maki 53, iri daya da na Barcelona wadda take ta biyu.

Tun a ranar Asabar, Barcelona ta koma ta biyu, bayan da ta je ta doke Sevilla 2-0 a wasan mako na 25 a gasar ta La Liga ta bana.

Atletico ce ta daya mai kwantan wasa da tazarar maki biyar tsakaninta da Barcelona da kuma Real Madrid.

Canjaras da Real ta tashi ranar Litinin ya kawo karshen cin wasa biyar a jere a dukkan karawar da ta yi a kwanan nan.

'Yan wasan Real Madrid da suka kara da Sociedad ranar Litinin:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da Mendy da kuma Chust.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modric da Casemiro da Valverde da Isco da kuma Arribas.

Masu cin kwallaye: Asensio da Lucas da Vini Jr da Mariano da Rodrygo da kuma Hugo Duro.