Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Schalke 04 ta kori kocinta, Gross kuma na hudu a kwanan nan
Ranar Lahadi Schalke 04 ta sanar da ta raba gari da kocinta, Christian Gross, bayan da ya kasa taka rawar gani da take bukata.
Haka kuma kocin bai bar kungiyar shi kadai ba har da daraktan wasanni, Jochen Schneider.
Ta kuma yi haka ne, bayan da Stuttagard ta doke Schalke 5-1 ranar Asabar a gasar Bundesliga.
Kungiyar tana ta karshen teburi a gasar kasar Jamus da maki tara a wasa 23 da koci hudu suka ja horar da ita a bana.
Kungiyar ta kori David Wagner, bayan jan ragamar wasa biyu, shima Manuel Baum ya kasa samar da abinda kungiyar ke fata.
Daga nan ne Huub Stevens ya karbi aikin rikon kwarya, sai kungiyar ta sanar da daukar Gross cikin watan Disamba.
Cikin wasa 11 da Gross ya ja ragamar Schalke 04 ta ci karawa daya tal da canjaras biyu da shan kashi a ffatawa takwas.