Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abun da ya kamata ku sani kan wasan Porto da Juventus
Juventus za ta ziyarci FC Porto a gasar Champions League wasan farko fafatawar zagaye na biyu da za su kara ranar Laraba.
Porto ba ta taba doke Juventus ba a karawa biyar baya da suka yi a gasar ta zakarun Turai, inda Juventus ta ci wasa hudu da canjaras daya.
Juventus ta kai wasan zagaye na biyu a gasar Champions League sau bakwai a jere, ita kuwa Porto wannan ne karo na hudu da ta kai wannan matakin a kaka biyar.
Kungiyoyin biyun sun fafata a wasan zagaye na biyu a Champions League a kakar 2016/17, inda Juventus ta kai karawar Quarter finals da ci 3-0 gida da waje.
Kungiyar Porto ita ce kadai ba a ci ba a gasar Champions League a gida a bana, ta kuma yi karawa biyar ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.
Tun lokacin da Cristiano Ronaldo ya fara buga wa Manchester United gasar Champions League a 2008, dan kwallon Portugal ya ci kwallo 62 a wasa 66 a karawar zagaye na biyu.
Jumulla, Ronaldo ya zura kwallo 67 a raga a karawa 81 a fafatawar zagaye na biyu a Champions League, kuma bakwai daga ciki a Juventus ya ci kwallayen.
'Yan wasan Juventus da za su kara da FC Porto:
Masu tsaron raga: Szczesny da Pinsoglio da kuma Buffon
Masu tsaron baya: Chielliini da De Light da Alex Sandro da Danilo da Bonucci da Demiral da Di Pardo da kuma Frabotta.
Masu buga tsakiya: Ramsey da Mckennie da Chiesa da Rabiot da Bentancur da Bernardeschi da Fagioli da kuma Kulusevski.
Masu cin kwallaye: Ronaldo da Morata da kuma Dybala.