Champions League: Kafar Liverpool daya ta kai Quarter finals

An wallafa

Liverpool ta sa kwazo ta doke RB Leipzig da ci 2-0 a Champions League karawar zagaye na biyu kuma wasan farko da suka kara ranar Talata.

Kungiyoyin biyu sun buga wasan ne a filin da ake kira Puska a Budapest, sakamakon dokar hana shiga Jamus da kasar ta kafa, don gudun yada cutar korona.

Mohamed Salah da kuma Sadio Mane ne suka ci wa kungiyar ta Anfield kwallayen da hakan ke nufin kafar Liverpool daya tana karawar daf da na kusa da na karshe.

Ranar 10 ga watan Maris, Liverpool za ta karbi wasa na biyu a Champions League da za su kece raini a Anfield.

Liverpool mai rike da kofin Premier League na fuskantar kalubale a bana, wadda take ta shida a teburin gasar bana.

Chelsea ce ta koma ta hudu, bayan da ta doke Newcastle United da ci 2-0 a makon nan, kuma West Ham ce ta biyar, bayan da ta caskara Sheffield United.