Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
David Alaba zai bar Bayern Munich a karshen kakar bana
David Alaba ya tabbatar cewar zai bar Bayern Munich a karshen kakar bana, bayan da suka kasa kulla sabuwar yarjejeniya a tsakaninsu.
Mai tsaron bayan dan kasar Austria ya koma kungiyar ta Jamus a 2008, ya kuma dauki lokaci suna tattaunawa a tsakaninsu don tsawaita zamansa a kungiyar.
Tun farko kunshin yarjejeniyar da Alaba da Bayern Munich suka kulla za ta cika ne a karshen kakar tamaula ta 2020/21.
Alaba, mai shekara 28, ya ci kwallo 33 a wasa 415 da ya yi wa Bayern, ya kuma lashe Champions League a kungiyar a 2013 da kuma 2020.
An dade ana alakanta Alaba da cewar zai koma buga gasar Premier League, wasu rahotannin na cewar Real Madrid ce za ta dauke shi domin ya dunga tsare mata baya daga tsakiya ko kuma daga gefe.
Alaba ya ci kofin Bundesliga tara tun lokacin da ya fara buga wa Bayern Munich tamaula cikin watan Fabrairu a lokacin yana da shekara 17 da haihuwa.
A makon jiya ya lashe kofin zakarun nahiyoyin duniya wato Fifa Club World Cup a Qatar da ya bai wa Bayern Munich damar lashe kofi shida a kakar tamaula.