Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Kounde, Haaland, Bremer, Neuhaus, Balogun, Ziyech, Raphinha

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce har yanzu yana sa ido kan Erling Braut Haaland, dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Norway mai shekara 20 bayan da kungiyar ta kasa dauko shi a bara. (MEN)
Atletico Madrid, da Juventus da Paris St-Germain na cikin manyan kungiyoyin da ke sha'awar raba Renato Tapia da kungiyarsa ta Celta Vigo. (AS - in Spanish)
Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce ya yi duka mai yiwuwa domin sayen Jamie Vardy, dan wasan gaba na Leicester City mai shekara 34 a 2016. (beIN Sport, via Star)
Da alama dan wasan tsakiya na Burnley da Kasar Ireland Robbie Brady, mai shekara 29 na iya komawa Celtic. (Mirror)
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya gargadi matasan 'yan kwallo na kungiyar da su shirya samu kalubale da tafiya wasu kungiyoyin a matsayin 'yan aro domin su nuna gogewarsu. (Goal)
Dan wasan gefe na Chelsea da Moroko Hakim Ziyech mai shekara 27, na tunani kan inda zai nufa bayan da ya kasa burgewa bayan ya baro Ajax. (Corriere Dello Sport - in Italian)
Manchester United na son hada Bruno Fernandes, mai shekara 26, da Raphinha tsohon abokin wasansa a Sporting Lisbon. (MEN)
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ce ya sanar da kungiyarsa yana bukatar a sayo wani sabon dan wasa a watan Janairun da ya gabata amma masu kungiyar sun ce ba za su sayi Eric Garcia, dan wasan baya na Manchester City mai shekara 20 ba . (Marca, via Mail)
Sai Arsenal ta biya fam miliyan 22 idan tana son sayen Dani Ceballos, dan wasan tsakiya mai shekara 24 daga Real Madrid. (Mirror)
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce bai cire ran zama kocin kasar Faransa ba wata rana a shekaru masu zuwa. (ESPN)










