Fitattun ‘yan wasan kwallon kafa da kwantiraginsu zai kare a bana

An wallafa

Wasan kwallon kafa ya ci karo da koma baya a fadin duniya tun bayan bullar cutar korana a bara.

Hakan ya sa aka fara dakatar da dukkan wasanni domin gudun yada annobar daga baya aka ci gaba da fafatawa amma ba 'yan kallo.

Cikin kalubalen da cutar ta haddasa har da matsin tattalin arziki da kungiyoyi suka fada, wadanda suka dunga rage albashin 'yan wasa da jami'ai da sauran matakan matse bakin aljihu.

Hakan ne ya sa kungiyoyi ke kasa sayen 'yan kwallo kudi da yawa kamar yadda ake yi a baya a lokacin cinikayyar 'yan wasan tamaula.

Ko lokacin da aka ci kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan Janairu, kungiyoyi sun fi zabar tsarin karbar aron dan kwallo maimakon su saya ya zama mallakinsu.

A karshen kakar bana ake sa ran karkare wasannin gasar nahiyoyi a wasu kasashe a Turai da sauran wurare.

Sai dai kuma kawo yanzu akwai wasu fitattun 'yan wasa da yarjejeniyarsu za ta kare a karshen kakar nan da ya kamata su ci gaba da taka leda.

Cikin 'yan kwallon nan BBC ta hada 'yan wasa 11 da za su iya gagarar kowacce kungiya suka hadu da iya.

Gianluigi Donnarumma (AC Milan)

AC Milan na taka rawar gani a gasar Serie, yayin da mai tsaron ragarta Gianluigi Donnarumma ya kama gola sama da sau 200 tun bayan da ya fara buga mata tamauala yana mai shekara 16.

Yanzu yana da shekara 21 da haihuwa kuma daya daga fitattun masu tsaron raga a duniya da ake cewar zai kai fam miliyan 50 kudin sayen shi.

Sai dai kuma Milan ta yi shiru kan batun tsawaita zamansa a kungiyar.

Wasu masu tsaron raga da kwantiraginsu zai kare a bana Fernando Muslera da Lukasz Fabianski da Sergio Romero da kuma Asmir Begovic.

Jerome Boateng (Bayern Munich)

Boateng wanda ya lashe kofin duniya da tawagar Jamus na buga wa Bayern Munich wasa sosai a bana.

Tsohon dan wasan Manchester City mai shekara 32 ya amince zai ci gaba da zama a Jamus amma har yanzu kungiyar ba ta zauna da shi ba kan tsawaita zamansa ba.

Sergio Ramos (Real Madrid)

Kyaftin din Real Madrid ya kusan buga wa kungiyar wasa 700 da cin kwallo 100.

Cikin watan Mais zai cika shekara 35, kuma Real Madrid ta yi masa tayin tsawaita kwantiraginsa kaka daya.

Sai dai wasu rahotanni na cewar kungiyar ta ce za ta rage albashinsa daga fam miliyan 10.5 zuwa fam miliyan 8.8

David Alaba (Bayern Munich)

Alaba shi ne na biyu mai tsaron baya da ake cewar zai bar Bayern Munich a bana, bayan da suka kasa cimma yarjejeniyar tsawaita zamansa.

Mai shekara 28 wanda ke iya buga wasan tsakiya an yi ta alakanta shi da cewar Real Madrid zai koma a badi.

Har ma ake cewar Real za ta dunga bashi fam 204,000 a kowanne mako, bayan an fitar da haraji.

Wasu masu tsaron baya da yarjejeniyarsu zai kare a karshen kakar bana sun hada da Eric Garcia da Juan Bernat da Patrick van Aanholt da kuma Thiago Silva.

Fernandinho (Manchester City)

Mai shekara 35 da haihuwa dan kasar Brazil ya buga wa City wasa sama da 300 ya kuma lashe Premier League uku da FA Cup.

Sai dai watakila Pep Guardiola ya kawo wani matashin domin yam aye gurbinsa.

Shi kansa dan kwallon bai yanke makomarsa ba, shi ya sa wasu rahotannin ke cewar kungiyoyin kudancin Amurka na zawarcinsa.

Georginio Wijnaldum (Liverpool)

Georginio ya lashe Champions League da kuma Premier League a Liverpool.

Har yanzu dan kasar Netherlands, Wijnaldum bai saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ba, kuma ana cewa watakila shi ne na farko a kungiyar da ya lashe Champions da Lik zai bar Anfield a bana.

Mai shekara 30 ya dade yana mafarkin son yi wa Barcelona wasa wadda Ronald Koeman ke horarwa.

Memphis Depay (Lyon)

Manchester United ta bai wa Depay damar gwada sa'a a Faransa tare da Lyon wadda kwantiragin da suka kulla ta shekara hudu za ta kare a karshen kakar bana, amma har yanzu bas u cimma matsaya ba.

Mai shekara 26 dan kasar Netherlands ana ta alakanta shi da zai koma Barcelona, yayin da Borussia Dortmund ke son zawarcin dan kwallon.

Julian Draxler (Paris St-Germain)

Yarjejeniyar dan kwallon tawagar Jamus, Draxler zai kare a Paris St German a karshen kakar bana.

Mai shekara 27 ya fada cewar zai karkare kwantiraginsa a PSG, zai kuma sanar da inda zai koma a cikin watan Maris.

Wasu masu buga tsakiya da kwantiraginsu zai kare a bana sun hada da Hakan Calhanoglu da Henrikh Mkhitaryan da Javi Martinez da kuma Juan Mata.

Angel di Maria (Paris St-Germain)

Di Maria bai ji dadin zaman da ya yi a Manchester United ba, amma yana taka rawar gani a Paris St Germain, wanda ya lashe Ligue 1 hudu da kai wa karawar karshe a Champions League a bara.

Dan wasan ya yi shiru duk da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar bana.

Lionel Messi (Barcelona)

A karshen kakar nan yarjejeniyar kyaftin din Lionel Messi zai kare a Barcelona.Tun farkon kakar bana Messi ya nemi izinin barin Camp Nou, bayan da kungiyar ta kasa taka rawar gani a bara da rigingimu da suka faru a kungiyar.

Tuni dai Manchester City ta nuna sha'awar daukar dan kwallon.

Sergio Aguero (Manchester City)

Aguero wanda shi ne ke kan gaba a cin kwallaye a Etihad a tarihi na fama da jinya a kakar bana.

Wasu rahotanni sun ce an bukaci dan kwallon mai shekara 32 da ya raba albashinsa biyu na fam 260,000 a kowanne mako idan har yana son ya ci gaba da taka leda a kungiyar.

Wasu fitattun masu cin kwallaye da kwantiraginsu zai kare a bana sun hada da Zlatan Ibrahimovic da Olivier Giroud da Stevan Jovetic da kuma Troy Deeney