Luiz Suarez ya doke tarihin cin kwallon Ronaldo a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Litinin Atletico Madrid ta tashi wasa 2-2 da Celta Vigo a karawar mako na 22 a gasar La Liga.
Tsohon dan wasan Liverpool da Barcelona, Luis Suarez shi ne ya ci mata kwallayen.
Kwallon da ya ci ya sa ya haura tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo a lokacin da ya taka leda a Sifaniya.
Kawo yanzu Luis Suarez ya ci kwallo 16 a wasa 17 da ya buga a kakar bana ta La Liga tun bayan da ya koma kungiyar daga Barcelona.
Tsohon dan wasan Ajax da Liverpool shi ne na farko da ya ci kwallo 16 a wasa 17 a La Liga a kani na 21.
A baya Cristiano Ronaldo ne ke rike da wannan tarihin na zura kwallaye 15 a wasa 17 a La Liga a lokacin da ya taka leda a Real Madrid, wanda ya koma Juventus daga baya.
Atletico wadda ke da kwantan wasa daya tana jan ragamar teburin La Liga da maki 51, sai Barcelona ta biyu mai maki 43, sannan Real Madrid mai maki iri daya da na kungiyar Camp Nou.







