Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Yan wasan Real Madrid sun yi rauni sau 38 kawo yanzu a kakar bana
Real Madrid na Ƙara fuskantar Ƙalubale a kakar bana, bayan da 'yan wasanta da dama ke yin jinya kawo yanzu.
Real Madrid wadda take riƘe da La Liga, ba ta kare kofinta na Spanish Super Cup ba a shekarar nan, an kuma yi waje da ita a Copa del Rey.
Kungiyar ta mayar da hankali kan lashe La Liga wanda take ta uku a kan teburin wasannin bana da kuma Champions League da za ta kara da Atalanta cikin watan Fabrairu.
To sai dai da yawan 'yan kwallon Real Madrid na fama da jinya da hakan zai iya zama barazana kan ƙoƙarin da take na ganin ta tsira da kofi a kakar nan.
Ranar Asabar likitoci suka yi wa kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya kuma bi sawun masu jinya da suka hada da Eden Hazard da Rodrygo da Dani Carvajal da kuma Fede Valverde.
Ranar Talata Real Madrid za ta kara da Getafe, kuma tuni ake cewa da ƙyar ne idan Alvaro Odriozola da kuma Eder Militao za su buga karawar saboda jinya.
Kimanin ƴan kwallon Real Madrid ke jinya kuma Toni Kross na hutun hukuncin
Sau 38 'yan wasan Real Madrid 20 suka yi rauni a kakar bana mai cike da kalubale.
Daman Real Madrid ba ta dauki dan kwallo ba a kakar 2020/21, kuma cutar korona ta kawo tsaiko da ta kai ana buga wasanni da yawa a karamin lokaci.