Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Andre Onana: An dakatar da mai tsaron ragar Ajax da Kamaru daga tamaula tsawon shekara daya
An dakatar da mai Tsaron ragar Ajax kuma dan kasar Kamaru, Andre Onana, daga harkokin kwallon kafa na tsawon shekara daya saboda shan kwaya.
An yi wa dan wasan mai shekara 24 gwaji a watan Oktoba, lokacin da ba a wasa, kuma a lokacin ne aka gano sinadarin furosemide a fitsarinsa.
Kungiyarsa ta Ajax ta ce Onana ya sha kwayar magani ce wadda aka rubuta wa matarsa bisa kuskure lokacin da ya ji ba shi da lafiya.
Onana da Ajax za su daukaka kara a kotun sauraron kararrakin wasanni game da dakatarwar da Uefa ta yi masa.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na zumunta, Onana ya ce ya yi kuskuren shan maganin da aka rubuta wa matarsa a matsayin aspirin sanoda kwalinsu "kusan iri daya ne, sannan ya kira dakatarwar da cewa 'mai tsauri".
"Duk abin ya faru ne sakamakon kuskure irin na dan Adam," in ji shi.