Europa League: Ajax ta yi kuskuren cire Haller daga tawagar da za ta buga mata gasar

An wallafa

Kungiyar Ajax ta yi kuskure ba ta sa sunan dan kwallon da ta dauka mafi tsada a tarihinta, Sebastien Haller, cikin wadanda za su buga mata Europa League ba.

Kungiyar ta Netherlands ta sayi dan wasan na Ivory Coast mai shekara 26 sama da fam miliyan 20 daga wajen West Ham United a watan Janairu.

Ranar Talata wa'adin mikawa nahiyar Turai 'yan wasa 25 da za su buga wa kowace kungiyar gasar Europa ya cika, kuma ba sunan Haller a Ajax.

Tuni dai dan wasan ya ci kwallo biyu a karawa shida da ya buga wa Ajax a kwanan nan.

Ajax za ta ziyarci Lille ta Faransa a wasan zagayen farko na kungiyoyi 32 da suka rage a gasar da za su kece raini ranar 18 ga watan Fabrairu.

Arsenal ta saka sunan dan kwallon da ta dauka aro daga Real Madrid, Martin Odegaard tare da mai tsaron raga Mat Ryan cikin wadanda za su buga mata wasannin.

Ita kuwa Manchester United wadda ta dawo buga gasar daga Champions League ta sa Amad Diallo mai shekara 18 cikin yan wasan da za su buga mata Europa League.

United ta kammala daukar matashin dan kwallon daga Atalanta ta Italiya.