West Ham ta sa kaimin daukar Jesse Lingard

An wallafa

West Ham ce kan gaba a zawarcin dan kwallon tawagar Ingila, Jesse Lingard daga Manchester United.

Lingard mai shekara 28 an bashi umarnin ya gwada sa arsa a wata kungiyar, bayan da Ole Gunnar bai amfani da shi sosai.

Wasu kungiyoyin da dama na son daukar Lingard, amma dai West Ham ce ta matsa ta kulla yarjejeni da Manchester United.

Sai dai kuma kafin cimma yarjejeniyar Lingard, sai West Ham sai ta dauki Craig Dawson ko kuma Said Benrahma.

Premier League ta kafa dokar da tace dole kungiya ta dauki dan wasan gida a kalla biyu da suke buga mata wasannin aron.

Dawson da kuma Benrahma sun je West Ham domin buga mata wasannin aro daga Watford da kuma Brentford masu buga Championship a watan Oktoba.

David Moyed ya yi aiki da Lingard a shekarar 2013 a Manchester United.