Barcelona za ta kalubalanci dakatar da Messi wasa biyu

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An dakatar da Kyaftin Lionel Messi daga buga wasa biyu, bayan da aka yi masa jan kati a wasan karshe a Spanish Super Cup.

Athletic Bilbao ce ta lashe Spanish Super Cup na bana, bayan da ta doke Barcelona 3-2 ranar Lahadi kuma kofi na uku da take da shi jumullla.

A karawar ce aka bai wa Messi jan kati, kuma na farko da ya taba karba, bayan sama da wasa 753 da ya buga wa Barcelona.

Alkalin wasa bai ga laifin da kyaftin din Argentina ya yi ba, amma na'urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR ita ta fayyace abinda ya faru.

Kwamitin da'a na hukumar kwallon kafar Spaniya shi ne ya wanke Messi da soso da sabulu cewar bai aikata laifin da gangan ba.

Ba dan haka ba da kyaftin din Barcelona ya fuskanci hukuncin dakatarwa wasa hudu har zuwa 12 da za a raba tsakanin fafatawar da zai yi a La Liga da sauran karawar cikin gida.

Hukuncin dakatar da Messi wasa biyu na nufin ba zai buga wa Barcelona Copa del Rey da za ta fafata da Cornella ba ranar Alhamis da wasan La Liga da Elhe.

Sau biyu aka bai wa Messi jan kati a lokacin da ya buga wa tawagar Argentina wasa da Hungary a 2005 da Copa America fafatawa da Chile a 2019.