Hazard zai buga wa Real Madrid wasa da Granada

Hazard

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta bayyana 'yan wasa 24 da za su fuskanci Granada a wasan cin kofin La Liga ranar Laraba, cikinsu har da Eden Hazard.

Rabon da dan kwallon tawagar Belgium ya buga wa Real tamaula tun raunin da ya yi a karawa da Alaves ranar 28 ga watan Nuwamba.

Hazard na fama da yawan yin raunin tun bayan da ya koma Real Madrid da taka leda daga Chelsea.

Sauran 'yan wasan da za su fafata da Granada har da Isco da kuma Vinicius Junior.

Sai dai Real za ta buga karawar ta ranar Laraba ba tare da Luca Modric ba, wanda ya yi rauni a wasan da Madrid ta yi nasara a kan Eibar da ci 3-1 ranar Lahadi.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Atletico mai jan ragama.

Ita kuwa Granada tana matsayi na bakwai da makinta 21.

Wannan layi ne

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Thibaut Courtois da Andriy Lunin da kuma Diego Altube.

Masu tsaron baya: Dani Carvajal da Eder Militao da Sergio Ramos da Raphael Varane da Nacho Fernandez da Marcelo da Alvaro Odriozola da kuma Ferland Mendy.

Masu buga tsakiya: Toni Kroos da Casemiro da Fede Valverde da Martin Odegaard da kuma Isco.

Masu cin ƙwallaye: Eden Hazard da Karim Benzema da Marco Asensio da Lucas Vazquez da Luka Jovic da Vinicius Junior da Mariano Diaz da kuma Rodrygo Goes.