Camp Nou: Shin ko filin wasan Barcelona ya zama huhun ma'ahu ne?

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Filin wasa na Barcelona da ake kira Camp Nou a baya wuri ne da duk kungiyar da ta ziyarta fatan ta bai wuce kar a zura mata kwallaye da yawa ba.

Ba wadda take tunanin idan ta je za ta samu makin da za ta tsira da shi, domin za a gara mata tamaula, sannan a zura mata kwallo ko kwallaye a Camp Nou.

Sai dai kuma a kakar bana filin Barcelona ba ya bai wa kungiyoyi tsoro, hakan ne ya sa duk wadda ta je can buga tamaula take zagewa ta taka leda.

Wannan ne ya sa kungiyar ta Camp Nou ke fama da kalubale a wasannin da take yi a gida a kakar bana.

Kawo yanzu Barcelona ta buga wasa 11 a gida da ya hada da La Liga da kuma Champions League a kakar shekarar nan.

Cikin wasannin gida da ta yi a shekarar nan, an doke ta sau biyu, shi ne wanda Real Madrid ta samu nasara da ci 3-1 ranar 24 ga watan Oktoba a gasar La Liga.

Sai kuma wanda Juventus ta doke ta a gasar Champions League da ci 3-0 ranar 8 ga watan Disamba.

Wasan da aka yi nasara a kan Barcelona a gida a gasar Zakarun Turai a baya shi ne a 2012/13 da Bayern Munich ta yi nasar da ci 3-0.

Haka kungiyar ta Camp Nou ta yi canjaras biyu a gida da wanda ta yi da Sevilla ranar 4 ga watan Oktoba da Valencia ranar 19 ga watan Disamba duk a gasar La Liga.

Wannan kakar ta tamaula ta bana daya ce daga mafi muni da Barcelona ke fuskanta cikin shekara 10.

Za ka iya kwatanta kakar 2016/17 da Barcelona ta yi canjaras uku da rashin nasara a dukkan karawa, inda ta kammala a mataki na biyu a gasar La Liga da Real Madrid ta lashe kofin.

A kuma wasannin Champions League a dai kakar, Barcelona ta yi ban kwana da gasar a karawar daf da na kusa da na karshe.

Ko da yake wasu na danganta rashin kokarin kungiyoyi a wannan lokacin saboda rashin magoya baya, duk da haka ba kungiyar da ke tsoron buga wasa da Barcelona a Camp Nou a yanzu.

Haka kuma Barcelona na kasa cin kananan kungiyoyin da a baya take tafiyar ruwa da su kamar su Levante ga kuma Cadiz da dai sauransu.

Kakar da Barcelona ba ta yi kokari ba a wasannin da ta buga a gida ita ce ta 2015/16 da kuma ta 2016/17.