Liverpool da Tottenham za su fafata ranar Laraba a gasar Premier League

An wallafa

Ranar Laraba Liverpool za ta karbi bakuncin Tottenhma a wasan mako na 13 a gasar Premier League da za su kara a Anfield.

Tottenham ce ta daya a kan teburin gasar bana da maki 25, Liverpool ce ta biyu mai maki iri daya da na Tottenham.

Abubuwan da ya kamata ku sani kafin wasan Liverpool da Tottenham a Anfield.

Yadda kungiyoyin suka kara a tsakaninsu

Wasa daya Liverpool ta yi rashin nasara daga 15 a Premier League haduwar baya-bayan nan da Tottenham ta ci 10 da canjaras hudu.

Cikin wasa 26 a baya da Tottenham ta ziyarci Anfield a Premier League sau daya ta doke Liverpool shi ne cikin watan Mayun 2011.

Tottenham ta yi rashin nasara a wasa biyar a jere da Liverpool a dukkan fafatawa da suka yi, idan aka kara doke ta zai zama karon farko ta sha kashi sau shida a jere.

Kwazon da Liverpool ke yi

Liverpool ta barar da maki 11 da ya kamata ta samu a kakar bana, bayan buga wasa 12. A bara sai da yi fafatawa 35 da ta kai yin asarar maki 11.

Kungiyar Anfield ta lashe dukkan wasa shida da ta yi a Anfield a bana da cin kwallo 18 aka zura mata shida a raga.

Har yanzu ba a doke Liverpool a wasan gida ba a Premier League tun rashin nasara a hannun Crystal Palace da ci 2-1 a Afirilun 2017. Ta buga wasa 65 kenan da cin 54 da canjaras 11.

Liverpool ta yi nasara a wasa 10 a gida a Premier League a fafatawa da wadanda suke shidan farko a kan teburin Premier League.

Kungiyar Anfield ita ce kadai ta zura kwallo a kowanne wasan Premier League da ta kara a bana.

Sadio Mane ya yi wasa bakwai bai ci kwallo ba a gasar Premier League a bana, kuma karon farko da ya dade bai zura kwallo ba a raga tun da ya koma Liverpool.

Liverpool ta yi nasarar cin fenariti 18 a gasar Premier League da take samu. Sunderland ce ta ci fenariti 23 a jere a gasar tsakanin Maris din 2021 zuwa Janairun 2017.

Kokarin da Tottenham ke yi

Tottenham ta ci wasa bakwai a Premier League da canjaras hudu, tun bayan rashin nasara a wasan farko a kakar bana a hannun Everton.

Ba a doke Tottenham a wasan waje shida da ta buga ba, ta yi nasara a hudu da canjaras biyu.

Tottenham ta hada maki 70 a karkashin Jose Mourinho tun da ya koma kungiyar - Manchester City tana da 75 sai Liverpool mai maki 90 sune ke gabansa.

Mourinho bai yi nasara a kan Klopp a wasa biyar a waje da suka fafata a dukkan karawa ba. Ya yi canjaras biyu da rashin nasara a wasa uku.

Wannan shi ne wasan waje da ya buga da yawa da bai samu sakamako ba a jere tun lokacin da ya zama kocin tamaula.

Harry Kane da Son Heung-min sun ci kwallo 12 a tsakaninsu a bana a Premier League, saura daya su yi kan-kan-kan da tarihin da Alan Shearer da Chris Sutton suka kafa a gasar a 1994-95.

A kwallo 24 da Tottenham ta zura a raga a bana, Son ya ci 10 da Kane mai tara.

Kane ya ci kwallo a wasa hudu baya da ya buga a Anfield, amma a karawar an yi canjaras biyu da shi da rashin nasara biyu a kwallayen da ya zura a raga.