Me kuke son sani kan Barca da PSG a Champions League

Barcelona vs PSG

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Ranar Litinin aka raba jadawalin wasannin zagaye na biyua a Champions League, inda Barcelona za ta kara da Paris St Germain.

Barcelona wadda ta kare a mataki na biyu a rukuni na bakwai za ta fafata da Paris St Germain wadda ta ja ragamar rukuni na takwas.

Barcelona ce za ta karbi bakuncin wasan farko ranar 16 ga watan Fabrairu a Camp Nou.

Paris St Germain za ta buga wasa na biyu da Barcelona a karawar kungiyoyi 16 ranar 10 ga watan Maris a Parc Des Princes da ke birnin Paris.

Wasannin baya da Barca da PSG suka fafata a tsakaninsu.

Karawar da ba za a manta da ita ba, ita ce kakar 2017 a lokacin da ake tunanin PSG ta fitar da Barca wadda ta ci 4-0 a Faransa.

A Spaniya Barca ta sa kwazon da ya kai ta zagayen gaba da yawan cin kwallaye 6-1, kuma har yanzu ana tuna fafatawar.

Sai dai kuma kungiyoyin sun hadu a wasanni da dama a Champions League da UEFA Super Cup Winners kuma yawanci Barca ce ke nasara.

A kakar 1995 ita ce tilo da PSG ta samu nasarar kai wa zagayen gaba a kan Barcelona.

Tarihin wasa tsakanin Barcelona da Paris St Germain

1994-95 Champions League karawar daf da na kusa da na karshe

Barca 1-1 PSG wasa na biyu PSG 2-1

(PSG ta kai zagayen gaba da cin kwallaye 3-2)

1996-97 Wasan karshe UEFA Cup Winners' Cup

Barca 1-0 PSG

2012-13 Champions League wasan daf da na kusa da na karshe

PSG 2-2 Barca wasa na biyu Barça 1-1 PSG

(Barca ta kai zagayen gaba da dokar cin kwallo a waje)

2014-15 Champions League karawar rukuni na shida

PSG 3-2 Barca wasa na biyu Barca 3-1 PSG

(Barca da PSG suka kai zagayen gaba)

2014-15 Champions League wasan daf da na kusa da na karshe

PSG 1-3 Bara wasa na biyu Barça 2-0 PSG

(Barca ta kai zagayen gaba da kwallo 5-1)

2016-17 Champions League wasan zagaye na biyu

PSG 4-0 Barca wasa Barca 6-1 PSG

(Barca ta kai zagayen gaba da cin kwallo 6-5)

Wadanda suka buga wasa a Barca yanzu suna PSG

Dan wasan da za a sa ido a karon farko da zai fuskanci Barcelona shi ne Neymar dan kwallon Brazil wanda ya koma Faransa da taka leda a 2017.

Wani dan kwallon daga Barcelona a PSG shi ne Rafinha wanda ya koma kungiyar cikin watan Oktoba da kuma Mauro Icardi wanda ya fara taka leda daga La Masia.

Neymar ya ci kwallo 9 a kakar bana a dukkan karawa, sai dai Kylian Mbappe ne kan gaba da 12 a raga.

Magoya bayan Barcelona sun kwan da sanin golan PSG, Keylor Navas da kuma Ángel Di María da suka buga wasa a Real Madrid suka fuskanci kungiyar ta Camp Nou..

Jadawalin zagayae na biyu a Champions League

  • Borussia Monchengladbach da Manchester City
  • Lazio da Bayern Munich
  • Atlético Madrid da Chelsea
  • RB Leipzig da Liverpool
  • Porto da Juventus
  • FC Barcelona da Paris St-Germain
  • Sevilla da Borussia Dortmund
  • Atalanta da Real Madrid