Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dogon Kyallu ne sarkin damben gargajiya na 2020
Dogon Kyallu ne ya lashe gasar damben gargajiya ta sarauta ta 2020, bayan da ya doko Ali Kanin Bello ranar Lahadi.
Dogon Kyallu ya yi nasara a kan Ali Kanin Bello daga Arewa a turmin farko a karawar da suka yi a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.
Wannan ne karon farko da Dogon Kyallu ya zama sarkin dambe kuma na uku a bangaren Guramada.
Garkuwan Cindo Guramada shi ne ya fara rike sarautar damben gargajiya a 2018, kuma shi ne ya yi tazarce a 2019.
Gasar 2020 ta ci karo da cikas sakamakon bullar cutar korona, bayan da wasu 'yan damben suka kasa halartar wasannin.
An kuma yi waje da wasu da dama a wasannnin bana, sakamakon halartar filin wasa a lokacin da ya kamata su buga dambensu.
A cikin watan Oktoba, Dogon Kyallu ya buge Ali Kanin Bello a wasan gasa, kuma kan a kare Ali Kanin Bello ya dauki fansa.
Mamman Bashar Danliti, shugaban kungiyar damben Najeriya reshen jihar Kano ya ce ''damben gargajiya wasan Bahause ne mai dimbin tarihi.''
"Ya kamata a yi masa gata da zai kara bunkasa domin 'yan baya su fahimci jarumtar da ake yi a wasan."
Danliti ya kara da cewar "Sai jama'a sun bayar da hadin kai shi ne wasan zai kara bunkasa a fadin duniya."
Bashar Sarkin masu shirya wasan damben gargajiya a Najeria ya kara da cewar "kowa ya bar gida gida ya bar shi, ya kamata masu ruwa da tsaki su shiga harkar yadda ya kamata."