Inter ta kasa taka rawar gani a Champions League tun tafiyar Mourinho

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Ranar 22 ga watan Mayun 2010 Inter Milan ta lashe kofin Champions League a Santiago Bernabeu, bayan da ta doke Bayern Munich 2-0.

Inter ta lashe kofin ne a karkashin jagorancin Mourinho, kuma a kakar ce kungiyar ta Italiya ta dauki kofi uku har da Serie A da kuma Coppa Italia, bayan Champions League..

Tun daga nan kungiyar ta kasa kare kambunta, inda Real Madrid ta lashe kofin tun daga nan Inter ta kasa yin wani abu a gasar kofin zakarun Turai.

A kakar 2010-11 Inter Milan ta lashe Supercoppa Italia da kuma Club World Cup tun daga nan kungiyar ba ta taka rawar gani ba.

Tun bayan da Mourinho ya bar kungiyar an samu wadanda suka maye gurbinsa da suka kasa daukar kofin Champions League.

Jerin wadanda suka horar da Inter suka kasa lashe Serie A balle Champions League.

Rafa Benitez da Leonardo da Gian Piero Gasperini da Claudoi Ranieri da Andrea Stramaccioni da Walter Mazzarri da Roberto Mancini da kuma Frank de Boer.

Sauran sun hada da Stefano Vecchi karo biyu da Stefano Pioli da Luciano Spalletti da kuma Antonio Conte.

Inter ta kasa kai wa zagaye na biyu a Champions League tun daga kakar 2010/11, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Marseille a wasan kungiyoyi 16.

Sakamako mai kyau da Inter ta samu tun bayan lashe Champions League a 2010, shi ne a kakar gaba da ta kai Quarter-Finals ta yi rashin nasara a hannun Schalke.

Daga nan kungiyar ta yi shiru ta kasa zuwa Champions League, amma a kakar 2018/19 kungiyar ta sake komawa gasar a karon farko.

Sai dai kaka uku a jere aka dunga fitar da Inter a wasannin cikin rukuni.

Sai dai kungiyar ta kai wasan karshe a Europa League, inda Sevilla ta doke ta.

A kakar bana kuwa Inter ta tsinci kanta a rukuni da ya kunshi Real Madrid da Borussia Dortmund da kuma Shakhtar Donesk.

Sai dai kungiyar ta zama ta karshe a rukuni na biyun da ta kasa samun gurbin Europa League.

Inter ta ci karo da cikas, bayan da ta kasa cin wasa uku a gida ta yi, sannan ta yi canjaras da Gladbach da Shakhtar, inda Real Madrid ta doke ta.

Kungiyar ta Italiya ta kashe Yuro miliyan 290 wajen sayo 'yan wasa a kaka biyu karkashin jagorancin Conte

Kuma fitattun 'yan wasan da take da su ya dace Inter ta kai karawar daf da ta karshe.

'Yan wasan da suka kware a tamaula a kungiyar sun hada da Achraf Hakimi da Romelu Lukaku da Alexis Sanchez da Christian Eriksen da Arturo Vidal da Nicolo Barella da kuma Stefano Sensi.