Neymar da Mbappe sun kai PSG zagayen gaba a Champions League

An wallafa

Paris St Germain ta kai zagayen gaba a gasar Champions League, bayan da ta doke Basaksehir da ci 5-1 ranar Laraba.

Neymar ne ya ci kwallo uku rigis a karawar, yayin da Kylian Mbappe ya ci biyu a wasan da suka buga a Faransa.

Basaksehir ta zare kwallo daya ta hannun Mehmet Topal a minti na 57.

Da wannan sakamakon PSG ce ta daya a rukuni na takwas da maki 12, sai RB Leipzig ta biyu itama da maki 12.

RB Leipzig ta kai zagaye na biyu ne, bayan da ta doke Manchester United da ci 3-2 ranar Talata a Jamus.

PSG da Basaksehir sun buga karawar ranar Laraba, maimakon Talata, bayan da aka samu korafin alkalin wasa mai jiran ko-ta-kwana ya yi kalaman wariya.

Hakan ne ya sa 'yan wasa suka fice daga filin, kuma tuni hukumar kwallon kafar Turai ta fara bincikar abinda ya faru.

Tuni dai Manchester United za ta koma buga gasar Europa League ta kungiyoyi 32.

Wannan ne karo na biyu da RB Leipzig ke kai wa mataki na biyu a jere a gasar Champions League.

Ita kuwa PSG ta buga wasan karshe da Bayern Munich wacce ta lashe kofin Gasar Zakarun Turan a bara.

Ranar Litinin ake sa ran fitar da jadawalin wasannin zagaye na biyu na kungiyoyi 16 a gasar ta Champions League.