Barcelonai: Kocin ƙungiyar Ronald Koeman ya soki shugabanta na riƙo kan sayar da Messi

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya soki shugaban riƙon ƙungiyar Carlos Tusquets bayan ya ce ya kamata a sayar da Lionel Messi a bazarar da ta wuce.
Tusquets ya ce ana "buƙatar" sayar da ɗan wasan, mai shekara 33, domin ƙungiyar ta Sifaniya ta samu kuɗi masu yawa.
Kwantaragin Messi zai ƙare a ƙarshen kakar wasan da muke ciki don haka zai iya barin ƙungiyar kyauta ba tare da an biya ko ƙwandala ba.
"Ban damu da abin da za a faɗa ba a wajen ƙungiyar. Amma yin magana irin wannan a cikin ƙungiyar ba zai taimaka wajen kwanciyar hankalin da muke buƙata ba domin yin aikinmu," in ji Koeman.
"Ba za mu iya hana abin da za a faɗa ba a wajen ƙungiyar, amma yin hakan a cikin ƙungiyar wani abu ne na daban."
Ɗan wasan Argentina Messi, wanda ya kwashe dukkan rayuwarsa ta tamaula a Barca, ya shaida wa mahukuntanta cewa yana son barin ƙungiyar a watan Agusta kuma ya ce zai iya tafiya ba tare da biyan ko sisi ba.
Amma mahukuntan Barcelona sun dage cewa ba haka batun yake ba, suna masu ƙarawa da cewa dole kyaftin ɗin nasu ya biya euro miliyan 700 idan yana so ya yi gaba.
"Idan akwai mutumin da ya kamata ya yanke hukunci kan makomarsa bai wuci Messi da kansa ba," a cewar Koeman.
"Mai yiwuwa sayar da Messi ra'ayin Tusquets ne na ƙashin kansa kuma ina martaba shi kan hakan, amma Messi yana da sauran shekara ɗaya da ta rage masa kuma shi ne zai yanke hukunci a kan hakan."









