Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Rudiger, Bissouma, Dembele, Tomori, Milik, Mourinho, Zaha, Williams

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal da Liverpool na duba yiwuwar sayo Yves Bissouma, dan wasan Brighton da kasar Mali ma shekara 24. (Talksport)
Dan wasan baya na Chelsea da Jamus Antonio Rudiger mai shekara 27, da kuma dan wasan baya na Ingila Fikayo Timori mai shekara 22 na iya sauya kungiyoyi a watan Janairu. Wasa daya kawai Rudiger ya buga wa kungiyarsa, inda shi kuma Timori ma bai buga ko wasa daya a kakar wasa ta bana. (ESPN)
Tottenham, Everton da Atletico Madrid na sa ido kan Arkadiusz Milik, dan wasan Napoli mai shekara 26. (AS)
West Ham za ta sayo Frederik Alves Ibsen, dan wasan baya mai shekara 20 daga Silkeborg kan fam miliyan 1.2 a watan Janairu. (Sky Sports)
Barcelona ta fara tattaunawa da Ousmane Dembele, dan wasa gaba na Faransa domin sabunta kwantiraginsa duk da sha'awar da Manchester United ke nunawa kan dan wasan mai shekara 23. (ESPN)
Ya kamata Manchester United ta kori kocinta Ole Gunnar Solksjaer kuma ta maye gurbinsa da Mauricio Pochettino, ko Antonio Cone ko Diego Simeone, inji tsohon mai kungiyar Crystal Palace Simon Jordan. (Talksport)
Wayne Rooney na ci gaba da nuna sha'awar zama kocin da dan wasa na din-din-din a kungiyar Derby County, duk da cewa tsohon dan wasan Ingila John Terry ma na sha'awar aikin. (Goal)
David Seaman tsohon dan wasan Arsenal, ya ba kungiyar shawarar sayo Wilfried Zaha, mai shekara 28 kuma dan wasan gaba na Crystal Palace da Ivory Coast. (Evening Standard)
Kocin Tottenham Jose Mourinho mai shekara 57 na ganin yana iya ci gaba da aikinsa na koci na tsawon shekara 15 zuwa 20 nan gaba. (i sport)










