Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasannin da Real Madrid za ta yi zuwa karshen shekarar 2020
Real Madrid za ta buga wasa bakwai kafin karshen shekarar 2020, ciki har da karawa shida a La Liga da daya a Champions League.
Madrid za ta karbi bakuncin Borussia Munchengladbach a wasan karshe a rukuni na biyu ranar 9 ga watan Disamba a karawar Zakarun Turai.
Kuma shi ne wasan da zai fayyace ko Real Madrid za ta kai zagayen gaba a gasar Champions League ta bana.
A rukuni na biyun Munchengladbach ce ta daya da maki takwas, sai Shakhtar da maki bakwai ta biyu, sannan Real Madrid itama da maki bakwai, inda Inter Milan take ta hudu da maki biyar.
Real za ta fara fafatawa da Sevilla ranar Asabar 5 ga watan Disamba a gasar La Liga karawar mako na 12.
Kwana hudu tsakani wato ranar 9 ga watan Disamba Real za ta buga Champions League da kungiyar Jamus a Spaniya.
Ranar Asabar 12 ga watan Disamba Real za ta buga wasan hamayya tsakaninta da Atletico Madrid a gasar La Liga.
Sai kwana uku tsakani Real ta karbi bakuncin Athletic Bilbao a filinta na Di Stéfano wato 15 ga watan Disamba a gasar Spaniya.
Daga nan Madrid za ta kece raini da Eibar ranar 20 ga watan Disamba ta kuma karbi bakuncin Granada 23 ga watan Disamba duk a wasan La Liga.
Real Madrid za ta buga wasa na karshe a shekarar 2020 a karawar La Liga, inda za ta ziyarci Elche ranar 29 ko kuma 30 ga Disamba.