Shakhtar Donetsk za ta karbi bakuncin Real Madrid a TUkraine

Real Madrid Shakhtar

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Real Madrid za ta ziyarci Shakhtar Donetsk domin buga wasa na biyar-biyar a cikin rukuni na biyu a Gasar Champions League ranar Talata.

A wasan farko da suka fafata ranar 21 ga watan Oktoba a Spaniya a gasar bana, Shakhtar ce ta yi nasara da ci 3-2.

Kungiyoyin biyu sun kara a gasar Zakarun Turai a tsakaninsu sau uku, inda Shakhtar ta ci fafatawa daya, ita kuwa Real ta yi nasara a biyu.

Haka kuma Madrid ta dura kwallo 10, yayin da aka zura mata shida a haduwa da ta yi da Shakhtar.

Damar da kungiyoyin rukuni na biyu suke da ita don kai wa zagayen gaba a Champions League:

Borussia Mönchengladbach ce ke kan gaba a wannan rukunin da maki takwas, sai Real Madrid ta biyu mai maki bakwai.

Shakhtar Donetsk tana ta uku da maki hudu, sai Inter Milan ta hudu ta karshe da maki biyu.

Sai dai kuma Mönchengladbach za ta kai zagaye na biyu a Champions League na bana idan ta doke Inter Milan a wasan da za su kara ranar Talata a Jamus.

Kungiyar ta Jamus za ta je zagayen gaba idan ma ta yi canjaras, amma idan Shakhtar ba ta ci Real Madrid ba.

Kuma Mönchengladbach za ta ci gaba da zama ta daya a rukuni na biyu da zarar ta doke Inter, sannan Madrid ta yi rashin nasara a hannun Shakhtar.

Sai dai kuma Real Madrid za ta kai zagayen gaba da zarar ta doke Shakhtar a ranar Talata a Ukraine.

Da zarar kungiyar ta Ukraine ta yi rashin nasara a hannun Real to sai dai ta jira gasar badi.

Ita kuwa Inter za ta kare a mataki na hudu a rukuni na biyu da zarar ta kasa doke Mönchengladbach, sannan Real ta yi rashin nasara a Ukraine.