Barca 2-1 Dynamo: Barca ta ci wasa uku a cikin rukuni a Champions League

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Barcelona ta doke Dynamo Kiev da ci 2-1 a wasa na uku-uku a cikin rukuni a Gasar Champions League ranar Laraba.

Lionel Messi ne ya fara cin kwallo a bugun fenariti, sai Gerard Pigue ya ci na biyu, yayin da Dynamo ta zare daya ta hannun Viktor Tsygankov.

Kyaftin din Barcelona ya ci kwallo uku kenan a bugun fenariti a gasar Champions League ta shekarar nan.

Da wannan sakamakon Barcelona ta hada maki tara a wasa uku, da zarar ta yi nasara a karawar gaba za ta kai zagaye na biyu a gasar duk da sauwa wasa biyu na cikin rukuni.

Cikin fenaritin da Messi ya buga a gasar shi ne ya fara cin Ferencvaros a bugun fenariti a wasan farko a kakar bana da Barca ta yi nasara da ci 5-1 ranar 20 ga watan Oktoba.

Haka kuma kyafin din Argentina shi ne ya ci na biyu a bugun fenariti a karawar da Barca ta doke Juventus da ci 2-0 ranar 28 ga watan Oktoba.

Kawo yanzu dan kwallon ya buga wasa tara a bana ya ci kwallo hudu kuma duk da bugun fenariti.

Messi ya fara cin fenatiri a kakar bana a wasan farko a gasar La Liga ranar 27 ga watan Satumba a karawar da Barca ta yi nasara a kan Villareal da ci 4-0.

Wannan ne wasa na tara da kungiyoyin biyu suka kece raini a tsakaninsu, inda Barca ta ci karawa shida, ita kuwa Dynamo ta yi nasara a uku.

Barcelona ta lashe kofin Champions League biyar a tarihi, sai dai rabon da ta dauka tun 2014/15. ita kuwa Dynamo Kiev ba ta da kofin kawo yanzu.

'Yan wasa 21 da Ronald Koeman ya fuskanci Dynamo Kiev a Camp Nou.

Ter Stegen da Dest da Pique da Sergio da Alena da Griezmann da Pjanic da Braithwaite da Messi da O. Dembele da kuma Riqui Puig.

Sauran sun hada da Neto da Lenglet da Pedri da Trincao da Jordi Alba da S. Roberto da F. De Jong da Ansu Fati da Junior da kuma Inaki Pena.

Sakamkon wasannin da aka buga a ranar Laraba:

  • Zenit St. Petersburg 1-1 Lazio
  • Basaksehir 2-1 Manchester United
  • Chelsea 3-0 Stade Rennais
  • Sevilla 3-2 FK Krasnodar
  • Club Brugge 0-3 Borussia Dortmund
  • Ferencvarosi 1-4 Juventus
  • RB Leipzig 2-1 Paris Saint-Germain