Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Geoffrey Kondogbia: Ya koma taka leda a Atletico Madrid a bana
Atletico Madrid ta sanar da daukar Geoffrey Kondogbia daga Valencia, ya kuma sa hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a 2024.
An amincewa Atletico ta dauki dan kwallon a wani tsari na gaggawa, bayan rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo, domin maye gurbin Thomas Partey wanda ya koma Arsenal.
Dan wasan mai shekara 27 ya koma Atletico nan take, kan kudi da ake cewar ya kai Yuro miliyan 15.
Ya fara sana'ar kwallon kafa a Lens wacce ya fara buga wa tamaula a 2010, mai buga tsakiya ya yi mata wasa 32 a Ligue 2 a kakar 2011/12 daga nan ya koma Sevilla.
Ya kuma buga wa Monaco wasa 64 a kaka biyu, ya kuma ci kwallo bakwai daga nan ya koma Inter Milan a 2015.
Bayan shekara biyu da ya yi a Italiya, inda ya buga karawa 56 a Inter ya ci kwallo biyu sai ya koma Valencia a 2017.
Kondogbia ya buga wa tawagar Faransa ta matasa 'yan shekara 16 wasanni, an kuma kirashi babbar tawagar sau biyar.
Daga baya ya koma yi wa kasar iyayensa wasa wato Afirka ta tskiya a 2018, wacce ya zama kyaftin, ya kuma buga mata wasa uku da cin kwallo daya.
Dan kwallon mai buga tsakiya zai taka leda a gurbi daya da Koke da Saul Niguez da Marcos Llorente da Hector Herrera da kuma Lucas Torreira a jagorancin Diego Simeone.