Eder Militao: Dan wasan Real Madrid ya kamu da cutar korona

An wallafa

Mai tsaron bayan Real Madrid, Eder Militao ya kamu da cutar korona, ba zai buga wa kungiyar Gasar Champions League da za ta kara da Inter Milan ba ranar Talata.

Dan kasar Brazil, mai shekara 22, ya killace kansa kamar yadda doka ta umarta, kafin daga baya a sake gwada shi, sannan ya koma taka leda idan ya warke.

Kungiyar ta Spaniya ta tabbatar da cewar Militao ne kadai ya kamu da annobar, bayan gwaji da ta yi wa masu horarwa da 'yan wasa da ma'aikata ranar Lahadi.

Real wacce ita ce ta karshe a teburin Champions League a rukuni na biyu, za ta karbi bakuncin Inter wacce take ta uku a teburin wasannin shekarar nan.

Militao ya buga wa Madrid wasa uku a kakar bana har da wasan farko a Champions League a fafatawar da Shakhtar Donetsk.

Real tana da maki daya tal a wasa biyu da ta yi a cikin rukuni na biyu, bayan da ta yi rashin nasara da ci 3-2 a gida a hannun Shakhtar da canjaras da Borussia Monchengladbach.