Jam'iyyun adawa: Wa'adin Alassane Ouattara ya ƙare

An wallafa

Shugabannin jam'iyyun adawa a Ivory Coast na cewa a gurinsu wa'adin Shugaba Alassane Ouattara tuni ya ƙare.

Suna magana ne bayan da aka yi wani zaɓe mai cike da takaddama, wanda shugaban ya tsaya takara domin zama shugaban kasar a wa'adi na uku.

Pascal Affi N'Guessan da Henri Konan Bedie sun ce Mista Ouattara ya karya dukkan dokokin kasar da suka ce sau biyu kawai mutum zai iya yin mulkin kasar, kuma sun yi kira ga 'yan kasar da su nuna fushinsu kan batun.

Mista N'Guessan ya ce ba a yi adalci ba a zaben:

"Akwai magudi da kura-kurai kan yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar na 31 ga watan OOktoba 2020, da hana wasu hukumomi masu yawa yin ayyukansu, da kuma rashin wasu rumfunan zabe, da kuma cewa fiye da kashi 90 cikin 100 na masu zabe ba su kada kuri'unsu ba."

Ya nemi jama'ar kasar da su kawo abin da ya kira "karshen kama karyar Mista Ouattara."

Ya kuma ce jam'iyyun siyasar kasar masu adawa da mulkin gwamnati mai ci na kira ga 'yan Ivory Coast da su hada kai da kungiyoyi masu kishin kasa da masu son adalci da zaman lafiya da su kawo karshen mulkin Mista Ouattara, "da cin amanar kasar da tsohon shugaba Alassane Ouattara ya aikata."

Jami'an tsaro a Ivory Coast sun ce an kashe a kalla mutum biyar kuma an raunata wasu masu yawa yayin wata hatsaniya da ta barke a ranar zaben.

Mista Ouattara ya sake tsayawa zabe ne bayan da mutumin da ya so ya gaje shi a mulki yayi mutuwar fuju'a a watan Yuli.

Su waye manyan 'yan takarar zaben shugaban ƙasar?

Alassane Ouattara, mai shakara 78, masanin tattalin arziki. Ya zama shugaban ƙasa a 2011, kuma ya yi nasarar kamamla wa'adinsa na biyu bayan ya shafe shekaru yana adawa da tsohuwar gwamnatin ƙasar. Jam'iyyarsa: Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP)

Henri Konan Bédié, mai shekara 86, tsohon dan siyasa. Ya taba mulkin kasar tsakanin 1993 da 1999, daga nan aka hambare shi daga mulki. Jam'iyyarsa: Democratic Party of Ivory Coast (PCDI)

Pascal Affi N'Guessan, mai shekara 67, tsohon dan siyasa. Ya taba rike mukamin firaminista tsakanin 2000 zuwa 2003 ƙarkashin tsohon shugaba Laurent Gbagbo. Jam'iyyarsa: Ivorian Popular Front (FPI) faction

Kouadio Konan Bertin, mai shekara 51, dan siyasa, wanda aka fi sani da sunan KKB, dan majalisar kasar ne mai takarar shugaban kasa mai zaman kansa.