Cristiano Ronaldo: Har yanzu kyaftin din Portugal na dauke da cutar korona

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Cristiano Ronado ba zai buga wa Juventus Gasar Champions League da za ta fafata da Barcelona ba, saboda har yanzu yana dauke da cutar korona.

Ronaldo ya soki yadda ake gwajin annobar, kuma tuni Juventus ba ta bayyana shi cikin wadanda za su buga mata Gasar ta Champions League ba ranar Laraba.

Mai shekara 35, ya killace kansa tun lokacin da ya kamu da cutar ranar 13 ga watan Oktoba, an kuma sake gwada shi kafin Labara.

Juventus ba ta ce komai ba kan ko kyaftin din tawagar Portugal na dauke da annobar a lokacin da aka yi masa gwajin.

Ronaldo ya fada a kafarsa ta sada zumunta cewar ''Ina ji na cikin koshin lafiya'' sannan ya caccaki yadda ake gudanar da gwajin cutar korona.

Sakamakon gwajin ya nuna cewar watakila wani na dauke da annobar ko akasin hakan.

Tsohon dan wasan Real Madrid ya shirya fuskantar Barcelona da abokin hamayyarsa Lionel Messi a karon farko tun bayan 2018 da ya bar Spaniya.

Wasan karshe da Ronaldo ya buga a bana shi ne wanda tawagar Portugal ta tashi 0-0 da ta Faransa ranar 13 ga watan Oktoba kan ya kamu da cutar.

Juventus za ta kara da Barca ba tare da mai tsaron baya Giorgio Chiellini da Matthijs de Ligt a karawar da za su buga a Turin, yayin da ake auna koshin lafiyar Leonardo Bonucci da kuma Paulo Dybala.

Juventus ta yi nasarar doke Dynamo Kyiv 2-0 a wasan farko na cikin rukuni a kakar bana.

Ita kuwa Barcelona za ta fafata da Juve ba tare da Philippe Coutinho, wanda ya yi rauni ranar Asabar a wasan El Clasico da Real Madrid ta yi nasara da ci 3-1 a Gasar La Liga.

Barcelona ta caskara Ferencvaros 5-1 a wasan farko na cikin rukuni a Gasar Champions League ta shekarar nan.