Mönchengladbach 2-2 Real: Hazard ya fara buga wa Real wasa ranar Talata

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Eden Hazard ya fara taka wa Real Madrid kwallo a bana ranar Talata a wasan da ta tashi 2-2 a gidan Borussia Monchengladbach a Gasar Champions League.

Tun kan hutu Borussia Monchengladbach ta ci kwallo biyu, bayan da aka kusan tashi ne Real ta farke ta hannun Benzema da Casemiro.

Real din wacce ta yi rashin nasara a gida da ci 3-2 a hannun Shakhtar Donesk tana da maki daya a wasa biyu da ta buga a bana.

Wannan ne karon farko da dan kwallon tawagar Belgium ya fara buga wa Real wasa a shekarar nan, sakamakon jinya da ya yi ta faman yi.

Dan wasan ya yi fama da jinya tun komawarsa Spaniya da taka leda, inda ya yi wa Real wasa 22 kacal a kakar 2019/20.

Cikin wadanda ke jinya a Real Madrid kawo yanzu sun hada da Dani Carvajal da Alvaro Odriozola da Nacho da Martin Odegaard da kuma Mariano.

Wannan shi ne wasa na uku da kungiyoyin suka fafata a Gasar ta Zakarun Turai, bayan da suka tashi 2-2 a gidan Real ranar 3 ga watan Maris, 1976.

A karawa ta biyu kuwa ranar 17 ga watan Maris a Borussia Mönchengladbach tashi suka yi 1-1.

Karawa tsakanin Real Madrid da Borussia Mönchengladbach a gasar:

Laraba 3 ga watan Maris 1976 EUROPEAN CUP

  • B M'gladbach 2 - 2 Real Madrid

Laraba 17 ga watan Maris 1976 EUROPEAN CUP

  • Real Madrid 1 - 1 B M'gladbach

'Yam wasan Real Madrid 21 da aka je da su Jamus:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Sergio Ramos da R. Varane da Marcelo da F. Mendy da kuma Santos.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.

Masu cin kwallo: Hazard, Benzema, Asensio, Lucas V., Jović, Vini Jr., and Rodrygo.

Wasa biyar nan gaba da Real Madrid za ta fafata:

Asabar 31 ga watan Oktoba La Liga

  • Real Madrid da Huesca

Talata 3 ga watan Nuwamba Champions League

  • Real Madrid da Inter

Lahadi 8 ga watan Nuwamba La Liga

  • Valencia da Real Madrid

Lahadi 22 ga watan Nuwamba La Liga

  • Villarrea da Real Madrid

Laraba 25 ga Nuwamba Champions League

  • Inter da Real Madrid