Real Madrid 1-0 Real Valladolid: Vinicius Junior ne ya ci wa Real kwallon

An wallafa

Vinicius Junior ne ya ci wa mai rike da kofin La Liga, Real Madrid kwallon da ta doke Real Valladolid 1-0 ranar Laraba.

Da wannan nasarar, kungiyar da Zinedine Zidane ke jan ragama ta hada maki maki hudu a wasan La Liga biyu da ta buga a waje.

Wannan ne karon farko da ta buga gasar bana a gida inda ta hada maki uku a wasan mako na hudu a La Ligar.

Golan Valladolid, Roberto ya yi kokari sosai, inda ya hana kwallon da Federico Valverde da ta Luka Jovic da suka buga masa su shiga raga.

Bayan da kungiyoyin suka koma karawar zagaye na biyu ne Vinicius ya ci wa Real kwallon tilo.

Da wannan sakamakon Real tana mataki na daya a kan teburi tare da Getafe da Villarreal da kuma Valencia da kowacce keda maki bakwai-bakwai.

Tun kan wasan kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 22 da za su fuskanci Valladolid.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Modrić da Casemiro da Valverde da Ødegaard da kuma Isco.

Masu buga gaba: Benzema da Asensio da B. Mayoral da Lucas V. da Jović da Vini Jr. da kuma Rodrygo.

Wasu wasannin La Liga 10 da Real Madrid za ta buga nan gaba:

Lahadi 04 ga Oktoban 2020

  • Levante da Real Madrid

Lahadi 18 ga Oktoban 2020

  • Real Madrid da Cadiz

Lahadi 25 ga Oktobvan 2020

  • Barcelona da Real Madrid

Lahadi 1 ga Nuwambar 2020

  • Real Madrid da Huesca

Lahadi 8 ga Nuwambar 2020

  • Valencia da Real Madrid

Lahadi 22 ga Nuwambar 2020

  • Villarreal da Real Madrid

Lahadi 29 ga Nuwambar 2020

  • Real Madrid da Alaves

Lahadi 6 ga Disambar 2020

  • Sevilla da Real Madrid

Lahadi 13 ga Disambar 2020

  • Real Madrid da Atl Madrid

Lahadi 20 ga Disambar 2020

  • Eibar da Real Madrid