Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid da Valladoli: Ko Real Madrid za ta hada maki uku kuwa?
Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Valladolid a wasan mako na hudu a gasar La Liga da za su fafata ranar Laraba a Alfredo Di Stefano.
A kakar bara Real ta hada maki hudu a kan Valladolid, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 ranar 24 ga watan Agustan 2019 a karawar farko.
A wasa na biyu a La Liga da suka fafata a gidan Valladolid, Real ce ta yi nasara da ci 1-0 ranar 26 ga Janairun 2020.
Kuma Nacho Fernandez ne ya ci wa Real kwallon saura minti 12 a tashi daga wasan.
A kakar bana Madrid ta yi canjaras a gidan Real Sociedad ranar 26 ga watan Satumba, kwana shida tsakani ta je ta doke Real Betis da ci 3-2.
Tuni dai kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 22 da za su fuskanci Valladolid.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Modrić da Casemiro da Valverde da Ødegaard da kuma Isco.
Masu buga gaba: Benzema da Asensio da B. Mayoral da Lucas V. da Jović da Vini Jr. da kuma Rodrygo.
Wasu wasannin La Liga 10 da Real Madrid za ta buga nan gaba:
Lahadi 04 ga Oktoban 2020
- Levante da Real Madrid
Lahadi 18 ga Oktoban 2020
- Real Madrid da Cadiz
Lahadi 25 ga Oktobvan 2020
- Barcelona da Real Madrid
Lahadi 1 ga Nuwambar 2020
- Real Madrid da Huesca
Lahadi 8 ga Nuwambar 2020
- Valencia da Real Madrid
Lahadi 22 ga Nuwambar 2020
- Villarreal da Real Madrid
Lahadi 29 ga Nuwambar 2020
- Real Madrid da Alaves
Lahadi 6 ga Disambar 2020
- Sevilla da Real Madrid
Lahadi 13 ga Disambar 2020
- Real Madrid da Atl Madrid
Lahadi 20 ga Disambar 2020
- Eibar da Real Madrid