Liverpool ta hada maki uku a kan Chelsea a gasar Premier

An wallafa

Liverpool ta nuna da gaske take za ta kare kofinta na Premier League, bayan da ta doke Chelsea da ci 2-0 a Stamford Bridge ranar Lahadi.

A karawar ta mako na biyu a gasar, Liverpool ce ke rike da wasan fiye da Chelsea wacce aka korar mata mai tsaron baya Andreas Christensen.

Tun farko alkalin wasa Paul Tierney ya bai wa Christensen katin gargadi a ketar da ya yi wa Mane daga baya ya je ya kalli abinda ya faru a na'urar da take taimaka alkali yanke hukunci ta fayyace masa laifin na jan kati ne.

Daga nan ne Mane ya ci wa Liverpool kwallo biyun da ya ba ta damar hada maki ukun da take bukata, kuma golan Chelsea, Kepa ya yi kuskure mai girma..

Sadio Mane shi ne dan kwallon Liverpool na biyu da ya ci kwallo biyu a Premier League a Stamford Bridge, bayan Steve McManaman a Disambar 1995 da kuma Philippe Coutinho a Oktobar 2015

Chelsea ta samu bugun fenariti, inda Jorginho ya buga golan Liverpool Alisson ya hana kwallo shiga raga.

Sabon dan kwallon Liverpool, Thiago Alcantara wanda ya canji Jordan Henderson shi ne ya yi wa Timo Werner ketar da ta samu fenariti.