'Yan Madrid da suka je Sociedad wasan farko a La Liga

An wallafa

Tun daga ranar Asabar aka shiga karawar mako na biyu a gasar cin kofin La Liga kakar 2020-21.

A wannan makon ne Real Madrid ta fara wasanta na farko, inda ta ziyarci Real Sociedad ta kuma tashi canjaras.

Wannan ne karo na biyar da Real ta kasa cin wasan farko a La L;iga daga takwas baya da ta fafata.

Madrid ita ce ke rike da kofin bara, ita kuwa Sociedad ta kammala kakar da ta wuce a mataki na shida.

Sociedad da Real sun fafata sau uku a bara, inda Madrid ta yi nasara a karawa biyu ita kuwa Socied ta ci daya.

Sun fara ne da gasar La Liga a bara a Santiago Bernabeu, inda Real ta yi nasara da ci 3-1 ranar 23 ga watan Nuwambar 2019.

Ranar 6 ga watan Fabrairun 2020 kungiyoyin suka gwabza a Copa del Rey, inda Sociedad ta samu nasara da ci 4-3.

Haka kuma sun kara haduwa karo na biyu a La Liga a gidan Sociedad ranar 21 ga watan Janairun 2020, inda Real ta ci 2-1.

Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 22 da za su buga karawar ranar Lahadi a gidan Sociedad.

'Yan kwallon Real Madrid

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Ramos da Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Mendy.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Odegaard da Marvin da kuma Arribas.

Masu buga gaba: Benzema da Mayoral da Jović da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.