Pierre-Emerick Aubameyang: Kyaftin na Arsenal ya tsawaita kwangilarsa

Asalin hoton, Getty Images
Kyafin din Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang ya sanya hannu a sabuwar kwangilar shekara uku a kungiyar.
Dan wasan mai shekara 31 ya je Arsenal a watan Janairu na 2018 kuma ya ci kyautar takalmin zinare na Premier League a kakar wasa ta 2018-19.
"Ban taba nuna shakkar sabunta kwangilata ba," in ji shi.
"Na yi amanna da Arsenal. Za mu yi nasara tare. Muna da abubuwan ban mamaki a nan kuma na yi amannar cewa gaba za ta fi baya armashi a Arsenal."
Aubameyang ya ci kwallon da ta bai wa Arsenal nasara a karawarta da Fulham ranar Asabar, a wasansu na Premier na farko na kakar wasa ta bana.
Kazalika dan wasan na Gabon ya zura kwallo biyu a wasan karshe na gasar FA da suka fafata da Chelsea a watan Yuli, abin da ya bai wa Arsenal damar samun gurbi a gasar Europa ta kakar wasa mai zuwa.
"Yana da muhimmanci Pierre-Emerick ya zauna tare da mu," a cewar kocin Arsenal Mikel Arteta.







