Bournemouth ta dagula lissafin Leicester a gasar Premier

An wallafa

Bournemouth daya daga cikin 'yan ukun karshen teburin Premier ta doke Leicester City da ci 4-1 ranar Lahadi.

Jamie Vardy ne ya fara ci wa Leicester City kwallo a minti na 23 da fara wasa, kuma haka suka yi hutu an ci Bournemouth 1-0.

Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne Bournemouth ta kara kaimi ta farke kwallo ta hannun Junior Stanislas a bugun fenariti.

Minti daya tsakani Bournemouth ta kara na biyu ta hannun Dominic Solanke, sannan mai tsaron bayan Leicester Jonny Evans ya ci gida.

Saura minti uku a tashi wasa ne Dominic Solanke ya zura na hudu kuma na biyu da ya ci a wasan.

Leicester ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Söyüncü jan kati.

Da wannan sakamakon Bournemouth ta koma ta 18 a kasan teburi ta yi sama kadan kenan da maki 31.

Hakan na nufin tana da tazarar maki uku tsakaninta da Watford ta 17 da tazarar maki daya tsakaninta da Aston Villa da ta koma ta 19.

Ita kuwa Leicester City tana nan matakinta na hudu da maki 59, bayan da Chelsea ta baro da ita daga matsayi na uku.

Wannan sakamakon dama ce ga Manchester United mai maki 58 ta koma ta uku a kan teburi idan ta ci Southampton ranar Litinin.