Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta fara jin kanshin gurbin zakarun Turai na badi
Arsenal ta koma ta bakwai a kan teburin Premier League na bana, bayan da ta je ta doke Wolverhampton da ci 2-0 ranar Asabar a Molineux.
Daf da za a je hutu ne matashin dan wasan Arsenal, Bukayo Saka ya fara zura kwallo a raga, wanda kwanan nan ya tsawaita zamansa a Gunners.
Saura minti hudu a tashi wasa ne Alexandre Lacazette ya ci wa Arsenal kwallo na biyu kuma na 10 a wasa 32 da ya buga a kakar bana.
Da wannan nasarar Arsenal ta yi sama zuwa mataki na bakwai da maki 49, ita kuwa Wolverhampton mai maki 52 tana ta shida a wasannin bana.
Wannan shi ne wasa na hudu da Arsenal ta yi nasara a jere tun bayan da Brighton ta doke ta 2-1 ranar 20 ga watan Yuni a gasar ta Premier League.
Wadanda Gurners ta doke sun hada da Southampton 2-0 da Sheffield 2-1 da Norwich City 4-0 da wannan da ta je ta ci Wolverhampton.
Sai a ranar Talata Arsenal za ta karbi bakuncin Leicester, yayin da Wolves za ta ziyarci Sheffield United ranar Laraba.