Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Aubameyang, Sancho, Partey, Thiago, Mikel da Havertz
Dan wasan Arsenal da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, ya ce yarjejeniyar shekaru uku yake so da albashin fam £250,000 a mako idan har zai ci gaba da taka leda a kulub din. (ESPN)
Manchester United na tunanin hakura da dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho saboda ba za ta iya biyan sama da fam miliyan 50 ba kan dan wasan mai shekara 20. (inews)
Chelsea na tunanin dauko dan wasan baya na Villarreal da Spain Pau Torres, mai shekara 23, wanda Arsenal, Barcelona, Manchester City da Manchester United ke sha'awa. (Mail)
Arsenal da dab da dauko dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Ghana Thomas Partey inda ta lunka kudaden da dan wasan mai shekara 27 yake karba. (AS - in Spanish)
Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce dan wasan Sifaniya mai shekara 29 Thiago Alcantara, da ake alakantawa da Liverpool, yana son barin kulub din a wannan bazara. (Bild, via Mirror)
Chelsea ta fara tattaunawa da dan wasan Brazil Willian, mai shekara 31, kan sabunta kwantaraginsa. (Goal)
Dan wasan baya na Bayer Leverkusen Wendell ya ce abokin wasansa Kai Havertz yana son komawa taka leda gasar Premier. Dan wasan mai shekara 21 Chelsea da Manchester United aka ruwaito suna ribibinsa. (Guardian)
West Brom na son dauko tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea da Najeriya John Obi Mikel, wanda tun watan Maris yake zaune ba ya da kulub bayan ya baro kungiyar Trabzonspor. (Sky Sports)
Inter Milan na tunanin saye dan wasan gaba na Manchester United da Chile Alexis Sanchez da ta karba aro. (Goal)
Dan wasan tsakiya na Schalke da Amurka Weston McKennie, mai shekara 21, yana son komawa gasar Premier a kaka mai zuwa. (Sky in Germany, via Sky Sports)
Tottenham na son dauko dan wasan Napoli da Poland Arkadiusz Milik, mai shekara 26, amma kuma tana fuskantar kalubale daga Juventus. (Goal)
Fiorentina na son tsohon dan wasan Roma da Italiya Daniele de Rossi, mai shekara 36, ya karbi ragamar jagorantar kulub din a kaka mai zuwa. (Sky Sport Italia - in Italian)
Watford, Leeds da Celtic na son dauko dan wasan Croatia Branimir Kalaica, mai shekara 22, daga Benfica. (Mail)