Man City ta yi wa Phil Foden gargadi bisa karya dokar bayar da tazara

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Manchester City ta ja kunnen Phil Foden kan karya dokar bayar da tazara, bayan da aka dauki hotonsa yana buga kwallon rairayi daf da teku.
An dauki hoton dan wasan mai shekara 20 yana taka leda cikin wasu mutane a ranar Lahadi.
Dokar gwamnati ta umarci mutane su yi wasa ko atisaye idan har za su iya bayar da tazarar mita biyu tsakaninsu.
Kawo yanzu an amince wa 'yan wasan da ke buga gasar Premier da yin atisaye na hada jiki amma da matakan hana yada cutar korona.
An kuma umarci su dinga bayar da tazara a koda yaushe.
A watan jiya aka dauki hoton mai tsaron bayan Manchester City, Kyle Walker ya ziyarci iyalansa a Sheffield a lokacin dokar zaman gida.





