Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Ighalo, Gomes, Kurzawa, Rashica, Bakayoko

An wallafa

Manchester United tana son tsawaita zaman aron dan wasan Najeriya Odion Ighalo, mai shekara 30, wanda ta karbo daga Shanghai Shenhua. (Standard)

Fatan Arsenal na dauko dan wasan Faransa Layvin Kurzawa daga Paris St-Germain ya samu tagomashi saboda suna da tabbaci cewa Barcelona ba za ta dauki dan wasan mai shekara 27 ba. (Le10 Sport - in French)

Liverpool, Southampton da kuma RB Leipzig suna son dauko dan wasan Werder Bremen Milot Rashica, mai shekara 23, a yayin da kwantaragin dan kasar ta Kosova take shirin karewa a watan Yuni. (Bild - in German)

Manchester United ta yi tayin bai wa Angel Gomes, mai shekara 19, £300,000 duk mako a wani bangare na yarjejeniyar da za ta hana shi barin kungiyar ba tare da ko sisi ba a bazara -sannan su tabbatar wa dan wasan na Ingila cewa yana cikin tsare-tsaren kungiyar na nan gaba duk da sha'awar da take yi na sayo dan wasan Birmingham City Jude Bellingham, mai shekara 16 (Sun)

Kazalika Manchester United tana son dauko dan wasan Sunderland dan shekara 16 Joe Hugill, a yayin da su ma Arsenal, Tottenham, Wolves da Leeds suke zawarcin matashin dan wasan. . (Northern Echo)

Dan wasan Chelsea Tiemoue Bakayoko, wanda a halin yanzu yake zaman aro Monaco, yana son komawa AC Milan. Dan wasan mai shekara 25 ya kwashe kakar wasa ta 2018-19 yana zaman aro a San Siro.(Calciomercato - in Italian)

Liverpool da Manchester City suna zawarcin dan wasan KV Mechelen dan kasar Belgium mai shekara 17 Aster Vranckx.. (Mirror)

Manchester City ta ware euro 32m domin dauko dan wasan Marseille dan kasar Faransa Boubacar Kamara, mai shekara 20 (Le10 Sport - in French)

Roma tana son Arsenal ta biya ta wani bangare na albashin mako-mako na dan wasan Armenia Henrikh Mkhitaryan, wato £180,000 idan tana so ta mayar da zaman aron da yake yi ya koma na dindindin (ESPN)

Kocin Crystal Palace Roy Hodgson, mai shekara 71, zai samu damar jan ragamar kungiyar idan aka ci gaba da Gasar Premier, duk da fargabar da ake yi cewa sai ya killace kansa saboda cutar korona. (Mail)

Jurgen Klopp ya ki amsa amsa tayin jagorantar tawagar 'yan kwallon kafar Mexico a 2015 domin kawai ya samu damar zaman manajan Liverpool (Goal)