Ronald Koeman: Kocin Netherlands yana asibiti yana fama da ciwon kirji

An wallafa

An kai kocin tawagar kwallon kafar Netherlands, Ronald Koeman asibiti, bayan da yake fama da ciwon kirji.

Tuni likitoci suka duba lafiyar tsohon kocin Southampton da Everton mai shekara 57.

Koeman wanda ya buga wa Barcelona wasa 192 a lokacin da yake murza-leda zai bar asibiti ranar Litinin.

An kuma ce za a bashi hutu na 'yan kwanaki domin ya samu ya murmure cikin sauri.

Koeman ya ci wa kasarsa kwallo 14 a wasa 78 da ya buga mata, ya kuma zama mai horas da ita a cikin shekarar 2018.