De Bruyne 'zai bar Manchester City', Roma tana son karbo aron Sanchez

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 28, ya ce mai yiwuwa zai bar Manchester City idan ta tabbata cewa ba za a janye haramcin da aka yi wa kungiyar na buga Gasar Zakarun Turai ba, a cewar jaridar Manchester Evening News.
Roma tana son son karbo aron dan wasan gaba na Chile Alexis Sanchez. Dan wasan mai shekara 31 yanzu haka yana zaman aro a Inter Milan, daga Manchester United. (Sky Sport Italia, via Goal - in Italian)
KazalikaRoma tana so ta ci gaba da rike dan wasan Manchester United da Ingila Chris Smalling, mai shekara 30, wanda yake zaman aro a can zuwa kakar wasa ta gaba, in ji koci Paulo Fonseca. (ESPN)
Newcastleza ta soma zawarcin dan wasanBayern Munich da Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, idan Mauricio Pochettino ya zama sabon kocin kungiyar. (Mirror)
Wata kungiya da ba a bayyana sunanta ba ta mika wa Lille euro 85m don karbo dan wasan Nigeria Victor Osimhen. Liverpooldai tana son dauko dan wasan mai shekara 21, (Telefoot - in French)
Real Madrid tana shirin sayar da 'yan wasa akalla biyar a kakar wasa ta bana, cikinsu har da dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 30. (AS - in Spanish)
Paris St-Germain tana son dauko dan wasan Leicester da Nigeria Wilfred Ndidi, mai shekara 23. (ESPN)
Newcastle da West Ham suna cikin kungiyoyin Gasar Premier da suke son dauko dan wasan Real Madrid da Serbia Luka Jovic, mai shekara 22. (90min)
Leicester za ta yi zawarcin dan wasan Arsenal da Scotland Kieran Tierney, mai shekara 22, idan aka sayar da dan wasan Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23. (Express)
Barcelona zata iya sayar da dan wasan Uruguay Luis Suarez a bazarar da muke ciki inda aka ce kungiyoyi da dama na MLS suna sob sayo dan wasan mai shekara 33. (Marca)
Newcastle, Everton, West Ham da kuma Leicester suna sanya ido kan yanayin da dan wasan Manchester United da Ingila Jesse Lingard, mai shekara 27, yake ciki. (90min)
Southampton tana fatan dauko dan Reims dan kasar Faransa Axel Disasi, mai shekara 22. (Mail)











